16 Afirilu 2020 - 04:59
Iran : Taron “OPEC” Ya Haifar Da 'Da Mai Ido

Shugaban kasar ta Iran, Dr. Hassan Rauhani ya fadawa takwaransa na kasar Venezuela Nicholas Maduro cewa; Taron na kungiyar masu arzikin kasashen man fetur da wasu kasashen da basu cikin kungiyar amma suna da arzikin man fetur din, ya haifar da kyakkyawan sakamako.

(ABNA24.com) Shugaban kasar ta Iran, Dr. Hassan Rauhani ya fadawa takwaransa na kasar Venezuela Nicholas Maduro cewa; Taron na kungiyar masu arzikin kasashen man fetur da wasu kasashen da basu cikin kungiyar amma suna da arzikin man fetur din, ya haifar da kyakkyawan sakamako.

Shugban na kasar Iran ya kuma jaddada muhimmancin ci gaba da bunkasa alaka a tsakanin Tehran da kuma sauran kasashen da su ke mambobi a cikin kungiyar ta “OPEC” domin ganin an rage yawan man fetur din da ake fitar da shi zuwa kasuwannin duniya a kowace rana.

Har ila yau,shugaban kasar ta Iran ya shaidawa takwaransa na Venezuela cewa; Wajibi ne kasashen biyu su bunkasa alaka a tsakaninsu da taimakawa junansu musamman a wannan lokacin na corona.

A nashi gefen shugaban kasar Venezuela, Nocholas Maduro ya jinjinawa Iran, gwamnati da al’umma a yakin da su ke yi da cutar corona

Maduro ya kara da cewa a halin da ake ciki a yanzu dukkanin duniya ce take fama da matsalar cutar corona, don haka da akwai bukatar a yi aiki tare domin samun nasara akanta.


/129